Bangaren kasa da kasa: An bude babban dakin kayyakin tarihin musulunci ta hanyar internet, domin sanar da sauran al'ummomin duniya matsayin musulunci a tarihi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na arab online cewa; An bude babban dakin kayyakin tarihin musulunci ta hanyar internet, domin sanar da sauran al'ummomin duniya matsayin musulunci a tarihi. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan shafi na internet day a kebancin kayan tarihin musulunci, akwai hotuna na muhimman wurare da wasu muhimman abubuwa na tarihin musulunci suka faru a cikinsu, da hakan ya hada kufan wuraren a cikin hotuna masu motsi gami da cikakken bayani kan ahakikanin abin day a faru. Daga cikin irin wadannan abubuwa kuwa hard a wadanda tarihinsu ke komawa ga tarihin halifofin bani umayya da kuma bani Abbas gami da sarakunan fatiniyawa da Usmaniya.
399997