IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Taro Kan Tarihin Manzon Allah A Morocco

Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wani taro kan tarihin manzon Allah SAW a kasar Morocco, bisa mahangar wasu Amurkawa masana kan harkokin tarihin yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Atbati ta kasar Masar cewa; An fara gudanar da wani taro kan tarihin manzon Allah SAW a kasar Morocco, bisa mahangar wasu Amurkawa masana kan harkokin tarihin yankin gabas ta tsakiya. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Morocco ita ce ta shirya gudanar da wannan zaman taron kara wa juna ilimi, bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da taron ita ce bayyana wa sauran al'ummar musulmi da ma sauran al'ummomin duniya yadda masana masu bincike na Amurka suka iya gano hakikanin sira ta manzon Allah, tare da bayyana mahangarsu a kansa bisa tarihin rayuwarsa da suka sani bisa bincike da suka gudanar, inda suka bayyana shi da cewa shi mutum ne day a sha banban da dukkanin mutane ta fuskacin kyawawan dabi'unsa da hankalinsa gami da iliminsa.


399962