Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga mahiyoyin yada labarai na kasar Gyrgustan cewa; Cibiyar kula da harkokin musulunci da kuma kur'ani da aka bude a cikin 'yan kwanakin a birnin Beshkik fadar mulkin kasar, ta samu karbuwa a wajen matasan kasar. Shugaban cibiyar Mahmud Kashgari ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka bude wata babbar cibiyar addinin musulunci a duk fadin kasar, kuma al'ummar kasar musamman ma matasa daga cikinsu sun nuna matukar sha'awarsu da ayyukan da cibiyar yanzu haka ta fara gudanarwa, da hakan ya hada da shirya taruka na addinin musulunci, tare da wayar da kan matasa dangane da muhimmancin da ke tattare da yin koyi da tarbiyar musulunci.
400083