Bangaren al'adu da fasaha: Bangaren kula da harkokin addini da al'adu na Iran da ke kasar Rasha ya bayar d akyautar wasu littafai na addinin musulunci da kuma wasu kan tarihin Iran da kuma harshen farisanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kafofin yada labarai na kasar Rasha cewa; Bangaren kula da harkokin addini da al'adu na Iran da ke kasar Rasha ya bayar d akyautar wasu littafai na addinin musulunci da kuma wasu kan tarihin Iran da kuma harshen farisanci. A lokacin bayar da kyautar wasu daga cikin jami'an gwamnatin Rasha bangaren ma'aikatar ilimi sun samu halartar wajen, kamar yadda wasu daga cikin ma'aikatan dakunan karatu na wasu biranan Rasha suka samu halartar wurin. Bayanin ya ce babbar manufar mika wadannan littafai ita ce wadata dakin karatu na Moscow da littafai na addinin musulunci, da kuma na farisanci gami da tarihin Iran, domin wadata masu bincike da littafan da suke bukata ta wannan fuska.
400111