Bnagaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Auglo a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a wajen taron share fage na ministocin harkokin wajen kasashen musulmi ya bayyana cewa, dole ne duniyar musulmi ta zage dantse wajen shiga cikin dukkanin harkoki na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar OIC cewa; Babban sakataren kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi ta Akmaluddin Auglo a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a wajen taron share fage na ministocin harkokin wajen kasashen musulmi ya bayyana cewa, dole ne duniyar musulmi ta zage dantse wajen shiga cikin dukkanin harkoki na kasa da kasa. Ya ce a irin wannan zama da aka gudanar a shekarar da ta gabata an bijiro da shawarwari a rubuce, amma yanzu babban abin da ake bukata shi ne aiki da su, domin kuwa a cewars yin aiki da shawarwarin da aka bijiro da su a zaman da ministocin harkokin wajen kasashen musulmi suka gudanar a shekarar da ta gabata, zai ba kasashen musulmin damar a dama da su a cikin dukkanin harkoki ba tare da an danne hakkokinsu ba.
399992