IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa A Saudiyya

Bangaren kasa da kasa: An gudanar da gasar kur'ani ta kasa a kasar Saudiyya a birnin Riyad fadar mulkin kasar, wadda yarima Salman bin Abdulaziz yake jagoranta, kuma zai bayar da kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA cewa; An gudanar da gasar kur'ani ta kasa a kasar Saudiyya a birnin Riyad fadar mulkin kasar, wadda yarima Salman bin Abdulaziz yake jagoranta, kuma zai bayar da kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara. Rahoton ya ci gaba da cewa wanna shi ne karo na goma sha biyu da ake gudanar da irin wannan gasa, kuma an ware makudan kudade ga wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar. Wadanda suka zo na daya acikin dukkanin bangarori za su samu kayutar kudi lakadan har riyal dubu 600, haka nan kuma sauran wadanda suka samu matsayi na biyu da na uku zasu samu nasu kason wanda bai kai na farko ba.

400124