Bangaren al'adu da fasaha: An fara gudanar da taro kan wani fim da aka shirya kan gwagwarmayar al'ummomin Gaza da labanan a babban dakin taro na cibiyar yada al'adu ta Iran da ke birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An fara gudanar da taro kan wani fim da aka shirya kan gwagwarmayar al'ummomin Gaza da labanan a babban dakin taro na cibiyar yada al'adu ta Iran da ke birnin Tehran. Rahoton ya ci gaba da cewa an gudanar da taron ne domin gwada irin kokarin masu gwagwarmaya a Gaza da Labanan ke wajen fuskantar zalunci da danniya na Isra'ila a kan al'ummominsu. Taron ya samu halartar wasu daga cikin wakilan kungiyoyin gwagwarmaya na Gaza da Labanan, da kuma jakadan kasar Iran a Labanan. Wasu daga cikin masana kan harkokin fina-finai na kasashen larabawa da na musulmi ne suka bayar da shawar hada wani fim wanda zai bayyana hakikanin abin da ke faruwa musamman ma a wadannan yankuna na Labanan da Palastinu, da kuma irin gwagwarmayar da al'ummomin yankin ke yi domin kawo karshen mamayar yahudawan sahyuniya kan yankunansu.
400973