IQNA

Gwamnatin Girka Ta Ki Amincewa Da Ware Makabartar Musulmi A Athens

Bangaren kasa da kasa: Gwamnatin kasar Girka ta ki amincewa da batun ware makabartar musulmi a birnin Athens fadar mulkin kasar, duk da ware filin da aka yi a lokutan baya domin mayar da shi makabartar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran time turk cewa; Gwamnatin kasar Girka ta ki amincewa da batun ware makabartar musulmi a birnin Athens fadar mulkin kasar, duk da ware filin da aka yi a lokutan baya domin mayar da shi makabartar musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin shekara ta 2005 babbar majami'ar kasar ta amince dad a ware wani makeken fili mai fadin mita dubu uku murabba'i domin mayar da shi makabartar musulmi, amma gwamnatin kasar ta ki amincewa da hakan, inda take ta fakewa da wasu dalilai domin nuna wa musulmi uzurinta, daga cikin dalilan kuwa hard a cewa an ware filin domin gudanar da wani aikin na daban. Tun kimanin shekaru goma sha biyu da suka gabata ne 'yan majalisar dokokin kasar suka tattauna batun samara da masallaci ga musulmi, amma masu tsattsauran ra'ayi daga cikinsu suka ki amincewa da hakan.

400695