IQNA

Malazia Babbar Misali Ce Na Ci Gaba A Duniyar Musulm

Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren cibiyar yada al'adu da ilimin addinin musulunci ta ISESCO Abdulaziz Altuwaijari ya bayyana cewa; kasar Malazia babbar abin buga misali ce a duniyar musulmi wajen ci gaban ilimi da al'adu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; Babban sakataren cibiyar yada al'adu da ilimin addinin musulunci ta ISESCO Abdulaziz Altuwaijari ya bayyana cewa; kasar Malazia babbar abin buga misali ce a duniyar musulmi wajen ci gaban ilimi da al'adu. Al-tuwaijari ya bayyana hakan ne jiya a lokacin rufe taron da aka gudanar a birnin Kualalampur na kasar Malazia, inda aka zabi birnin matsayin birnin al'adun musulunci na shekara ta 2009 a nahiyar Asia. Ya ce dole ne a yaba wa kasar Malazia ta fuskacin himma da kwazon da take nunawa a dukkanin fuskoki na ci gaban ilimi da al'adu, kuma ta zama abin koyi ga sauran kasashen musulmi. A nasa bangaren ministan al'adu na kasar Malazia ya bayyana cewa yanzu haka ana gudanar da wani baje koli na kayyakin al'adu da fasahar musulunci a fagage 227 a kasar ta Malazia.

400732