IQNA

Za A Gudanar Da Taron Bahasi Kan Dalilan Rashin Gurbatar Kur'ani

15:08 - May 07, 2009
Lambar Labari: 1775200
Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da wani taro a birnin Istanbul na kasar Turkiya domin yin bahasi kan dalilai da ke tabbatar da cewa kur'ani mai tsarki baya karbar canji ko gurbata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Haber cewa; za a fara gudanar da wani taro a birnin Istanbul na kasar Turkiya domin yin bahasi kan dalilai da ke tabbatar da cewa kur'ani mai tsarki baya karbar canji ko gurbata. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Turkiya, tare da wasu jami'ai daga cibiyoyin ilimin addinin addini gami da malamai da kuma masana daga jami'oi daban-daban na kasar, inda za su tattauna muhimman batutuwa kan da suka shafi kur'ani da kuma dalilai da ke tabbatar da cewa shi littafi ne da baya karbar canji ko gurbata, shi ne kamar yadda aka safkar da shi tun farko, inda mahalarta taron za su gabatar da jawabai da makaloli kan hakan.

400781

captcha