IQNA

Filipine Na Kokarin Zama Mamba A Kungiyar Kasashen Musulmi

15:06 - May 07, 2009
Lambar Labari: 1775209
Bangare siyasa da zamantakewa; Shugabar kasar ta Filipines ce Goloriya Areyo ta bayyana cewa; kasarta tana iyakacin kokarin ganin ta shiga cikin kasashe mambobi a cikin kungiyar kasashen musulmi.
Daga yankin kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta nakalto daga jaridar Darul hayat ta Saudiya cewa Goloriya shugabar kasar Filipines na kokarin ganin kasarta ta shiga cikin jerin kasashe mambobi a cikin kungiyar OCI ta kasashen musulmi.Kuma hakan ya biyo bayan jan namijin kokarin da kasashen musulmi ke yi kan wajen tabbatar da sulhu a yankin.

400772
captcha