IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Mata A UAE

16:59 - May 09, 2009
Lambar Labari: 1775994
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta mata a birnin Abudahbi fadar mulkin kasar Hadaddiyar daulai larabawa, a babbar cibiyar gudanar da harkokin addinin musulunci ta birnin karkashin kulawar sarkin kasar Muhammad Bin Khalifa al nahyan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Albayan da ake bugawa a birnin Dubai cewa; An fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta mata a birnin Abudahbi fadar mulkin kasar Hadaddiyar daulai larabawa, a babbar cibiyar gudanar da harkokin addinin musulunci ta birnin karkashin kulawar sarkin kasar Muhammad Bin Khalifa al nahyan. Rahoton ya ci gaba da cewa yanzu haka dai sama da mata 57 ne suke karawa da juna a bangaren hardar kur'ani da kuma karatunsa a bangaren kirar tartil a cikin wannan gasa. A nata bangaren babbar diyar sarkin Hadaddiyar daular larabawa Shema Bint Khalid Ali Nahyan ta bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar mata wajen mayar da hanakali kan karatun kur'ani da harsarsa .


401661
captcha