IQNA

Za A Fara Bayar Da Horo Ga Limaman Masallatai A Austaria

Bangaren kasa da kasa: Jami'ar birnin Vienna na kasar Austria ta bayar da bayanin cewa nan da wani lokaci mai zuwa za ta fara bayar da horo na musamman ga limaman masallatai na kasar Austria, tare da basu shedar kammala karatu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar faransa AFP cewa; Jami'ar birnin Vienna na kasar Austria ta bayar da bayanin cewa nan da wani lokaci mai zuwa za ta fara bayar da horo na musamman ga limaman masallatai na kasar Austria, tare da basu shedar kammala karatu. Bayanin ya ce muhimman abubuwan da limaman za su samu horo a kansu sun hada da sanin sauran addinai musamman ma wadanda aka safkar daga sama, da kuma shari'a a zamanance gami da ilimin zamantakewa, ta yadda hakan zai taimaka musu wajen sanin al'adu daban-daban na al'ummomin kasar. Daga cikin sharuddan da dole ne wadanda zai halarci horon ya kasance yana da su har da cikakkiyar masaniya kan tauhidi a musulunce.


401652