IQNA

Za A Gudanar Da Taron Hadin Kan Musulmi A Turkiya

16:58 - May 09, 2009
Lambar Labari: 1776002
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taro kan hadin kan al'ummar musulmi a kari na uku a birnin Kuniya na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar za ta dauki nauyin gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Dunyabulteni cewa; Za a gudanar da taro kan hadin kan al'ummar musulmi a kari na uku a birnin Kuniya na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar za ta dauki nauyin gudanarwa. A wajen gudanar da taron za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi hadin kan ak'ummar musulmi da kuma rawar da masu isar da sakon addinin musulunci za su iya takawa wajen hada kan al'ummar musulmi. Haka nan kuma wadanda za su halarci taron za su yi dubi kan hanyoyin day a kamata abi wajen kara fadada ayyukan isar da sakon musulunci a sassa daban-daban na nahiyar turai. Hakan nan kuma a taron za a yi bahasi kan rubuce-rubucen babban malamin nan na kasar Turkiya Badi'u zaman, wanda ya rayu tun a cikin karni na 12, wato sama da shekaru 800 da suka gabata.


401599





captcha