Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwasat ta kasar Bahrain cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani da aka gudanar a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain mai taken Zikrulhakim.Rahoton ya ci gaba da cewa gasar ta samu halartar makaranta daga kasashen larabawa daban-daban, da suka hada da kasashen Saudiyya, Kuwait, Qatar, Pakistan da kuma mai masafkin baki Bahrain. Daga cikin wadanda suka samu halartar gasar akwai masu kanan shekaru da kuma masu shekaru matsakaita. An gudanar da gasar ne a bangarori daban-daban na karatun kur'ani da kuma kira'a gami da ka'idojin karatun kur'ani wato tajwid, haka nan kuma a bangaren hardar kur'ani an kasa gasar zuwa bangarori daban-daban, da suka hada da bangaren hardar dukkanin kur'ani.
401604