Bangaren kasa da kasa: Jakadan kasar Holland a kasar Indonesia ya yi kyawawan kalamai kan addinin musulunci, ya kuma yi kakkausar suka kan dan majalisar nan na kasar Holland mai tsananin gaba da addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Jakarta post cewa; Jakadan kasar Holland a kasar Indonesia ya yi kyawawan kalamai kan addinin musulunci, ya kuma yi kakkausar suka kan dan majalisar nan na kasar Holland mai tsananin gaba da addinin musulunci. Jakadan kasar ta Holand a Indonesia Windam, ya bayyana cewa addinin musulunci addini ne da ke taka rawa wajen ilmantar da al'umma tare da bata kyakkyawar tarbiya domin ci gaban rayuwa, kuma al'ummar Holand ba su gaba da addinin musulunci, domin kuwa a binda dan majalisar nan na kasar Holand Geert Wilders ke bay a wakiltar al'ummar kasar, kuma baya bayyana ra'ayinsu kan addinin musulunci da musulmi. A nasa bangaren Geert Wilders ya mayar da martini kan furucin na jakadan Holand a Indonesia, inda ya bayyana cewa abin kunya ne wani jami'in gwamnatin Holland ya yabi addinin musulunci da musulmi.
401614