Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran timeturk cewa; 'Yan majalisar dokokin jahar Hawai ta kasar Amurka sun amince ga baki daya kan ware ranar 24 ga watan satumba na kowace shekara a matsayin ranar addinin musulunci. Rahoton ya ce 'yan majalisa 22 ne suka amince da wannan daftarin kudiri, yayin da wasu uku suka ki amincewa da shi, tuni dai shugabar majalisar dokokin jahar ta rattaba hannu kan wannan kudiri, kuma za a mika shi ga gwamnan jahar domoin ita ma ta sa hannu kansa. Babban dalilin gabatar da wannan daftarin kudiri ne shi ne, yadda aka yi la'akari da cewa addinin musulunci addini ne mai tsawon tarihi da ci gaba a cikin addinai da aka safkar da su daga sama, wanda kuma ya kamata a ware masa rana ta musamman a kowace shekara.
401556