IQNA

Za A Gudanar Wani Zama Kan harkokin Kasuwanci A Musulunce

15:59 - May 10, 2009
Lambar Labari: 1776511
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani zama na musamman kan harkokin kasuwanci a mahangar musulunci a birnin Qazan na Tataristan, wanda shi ne irinsa na farko da za a gudanar a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Akhbar Alyaum cewa; Za a gudanar da wani zama na musamman kan harkokin kasuwanci a mahangar musulunci a birnin Qazan na Tataristan, wanda shi ne irinsa na farko da za a gudanar a kasar. Wannan taro zai samu halartar wakilai daga cibiyoyi daban-daban daga kasashen Rasha gabas ta tsakiya nahiyar turai da gabaci gami da kudancin Asia, gami dam asana daga jami'oin kasashen musulmi. Muhimman abubuwan da taron zai yi dubi akansu sun hada da batun fadada harkokin bankin musulunci, tare da karbar hannayen jari daga kasashen duniya daban-daban, tare da karfafa dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen musulmi da kuma sauran kasashe.

401933




captcha