IQNA

An Fara Bayar Da Horon Karatun Kur'ani A Kasar saudiyya

15:57 - May 10, 2009
Lambar Labari: 1776513
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wani shirin bayar da horon karatun kur'ani wanda shi ne karo na saba'in da biyar da ake gudanar da irinsa a birnin Ta'if na kasar saudiyya, wanda cibiyar kula harkokin kur'ani ta kasar ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAS cewa; An fara gudanar da wani shirin bayar da horon karatun kur'ani wanda shi ne karo na saba'in da biyar da ake gudanar da irinsa a birnin Ta'if na kasar saudiyya, wanda cibiyar kula harkokin kur'ani ta kasar ta shirya gudanarwa. Wannan shiri na bayar da horo yana daya daga cikin
muhimman shirye-shiryen kur'ani da wannan cibiya ke gudanarwa, wanda ya kan kwashe tsawon makonni shida a jere ana gudanar da shi. Daya daga cikin sharuddan yin rihista shi ne mutum ya kasance dan kasar saudiyya ne, kuma ana yin rijistan shiga cikin shirin bayar da horon kyauta ba tare da biyan wasu kudade ba.

401988

captcha