IQNA

An Yaba Da Ci Gaban Da Iran Ta Samu A Taron Tattaunawa Tsakanin Addinai

Bangaren siyasa da zamantakewa: shugaban kwamitin da ke shirya zaman tattaunawa tsakanin addinai Alexy Vokeen ya bayyana cewa irin ci gaban da Iran ta samu na daya daga cikin abubuwan da za a bijiro da su a wurin zaman tattaunawa tsakanin addinai da al'adun al'ummomin duniya da za a gudanar a nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata ziyara day a kai ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke birnin Moscow na kasar Rasha, shugaban kwamitin da ke shirya zaman tattaunawa tsakanin addinai Alexy Vokeen ya bayyana cewa irin ci gaban da Iran ta samu na daya daga cikin abubuwan da za a bijiro da su a wurin zaman tattaunawa tsakanin addinai da al'adun al'ummomin duniya da za a gudanar a nan gaba. Alexy ya bayyana hakan ne a lokacin ya ke zantawa tare da shugaban bangaren da ke kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin na Iran Abu Zar Ibrahimi Torkaman, inda ya tabbatar masa da cewa ko shakka babu batun ci gaban da Iran ta samu tafuskoki daban-daban musamman ta fuskacin al'adu, na daya daga cikin muhimmman abubuwan da za a bijiro da su a taron tattaunawa tsakanin al'adu da addinai da za a gudanar a cikin Oktoban shekara ta 2009 da muke ciki.

402190