IQNA

Al'ummar Palastinu Na Bukatar Rayuwa Cikin 'Yanci Kamar Sauran Al'ummomi

Bangaren siyasa: Dangane da batun tattara bayanai kan ayyukan ta'addanci da kisan kare dangi da yahudawan sahyuniya suka yi kan al'ummar palastinu, muna fatan a gudanar da wannan bincike cikin adalci da gaskiya, ta yadda al'ummar palastinu za su samu 'yancin kansu da walwala kamar sauran al'ummomin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na ma'akatar shari'a ta jamhuriyar musulunci ta Iran cewa; babban alkalin kotun kolin Iran Ayatollah Qorban Ali Najaf Abadi ya bayyana cewa; Dangane da batun tattara bayanai kan ayyukan ta'addanci da kisan kare dangi da yahudawan sahyuniya suka yi kan al'ummar palastinu, muna fatan a gudanar da wannan bincike cikin adalci da gaskiya, ta yadda al'ummar palastinu za su samu 'yancin kansu da walwala kamar sauran al'ummomin duniya. Babban alkalin kotun kolin kasar Iran din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mambobin kwamitin kasa da kasa na goyon baya da taimakon al'ummar palastinu a ofishinsa da ke birnin Tehran, ya ce muna fatan ganin kwamitin bincike kan ayyukan ta'addancin Isra'ila zai gudanar da bincikensa kamar yadda ya kamata kan adalci da kiyaye hakkokin palastinawa.

402227