Bangaren adabi: Mu'assasar Alhuda ta dauki nauyin fassara kur'ani da harshen turancin Ingilishi domin amfanin matasa, kuma tuni akafitar da shi a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Mu'assasar Alhuda ta dauki nauyin fassara kur'ani da harshen turancin Ingilishi domin amfanin matasa, kuma tuni akafitar da shi a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mu'assasa wadda daya ce daga cikin wadanda suka baje dimbin littafai a kasuwar baje koli da ake gudanarwa a birnin Tehran, ta fitar littafai sama da guda dari biyu wadanda aka buga da harshen farisanci, yayin da ta fitar da littafai kimanin dari hudu da goma sha daya da aka buga su a cikin harshen larabci, sai kuma littafai saba'in da shida da aka buga da harshen turanci, sai kuma wasu littafan da aka buga a cikin yaruka daban-daban, kamar harsunan Rashanci jamusanci Faransanci Hausa da dai sauransu.
402099