Bangaren al'adu da zamantakewa: An fara gudanar da wani taro da aka bai wa take makon palastinu a kasar Malazia, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria SANA cewa; An fara gudanar da wani taro da aka bai wa take makon palastinu a kasar Malazia, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa. Shugaban cibiyar Martinin ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan taron ita ce bayyana muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar palastinawa, ta yadda al'ummar kasar Malazia za su samu cikakkiyar masaniya kan halin da al'ummar palastinu suke ciki, da kuma wahalar da suke sha a hannun yahudawan sahyuniya, gami da bayyana wa al'umma irin muhimmancin da ke tattare da taimakon wannan al'umma maras kariya.
402017