Bangaren ilimi da al'adu: wani gungu na masu bincike yan Iraki sun kai ziyarar gani da ido ga mu'assisa ta darul Hadis da ke Iran bayan kammala taron Kuleini da aka gudanar.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna net a watsa rahoton cewa; wadannan masana sun kai wannan ziyarar gani da ido domin shadawa idonsu kan ayyukan da wannan cibiyar yada ilimi da al'adu na Musulunci ke gudanarwa a bangarori daban-daban . Sun bayyana gamsuwarsu kan yadda wannan mu'assisa ke tafiyar da ayyukanta cikin tsari da sanin makamar aiki.
402809