Bangaren kasa da kasa: A wani kauye da ke cikin jahar Chin Shiya a kasar Chana mai suna Shunkho da ke arewa maso yammacin kasar, an samu wani kur'ani da aka a dana shi har tsawon shekaru sama da 800, kuma har yanzu ana ci gaba da ajiye shi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; A wani kauye da ke cikin jahar Chinshiya a kasar Chana mai suna Shunkho da ke arewa maso yammacin kasar, an samu wani kur'ani da aka a dana shi har tsawon shekaru sama da 800, kuma har yanzu ana ci gaba da ajiye shi. Mazauna wannan kauyen dai wata kabila ne da ake kira Salar, kuma suan cikin marassa rinjaye a tsakanin kabilun da ke cikin kasar, domin kuwa adadinsu bai wuce dubu 100 ba. A wani masallaci da ke kauyen an samu kur'ani wanda aka bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru sama da 800 a wurin, domin kuwa shi kansa masallacin ya dauki tsawon lokaci na daruruwan shekaru, wanda ake lisafta shi daya daga cikin wuraren tarihin yankin. Wasu daga cikin masu bincike kan kufan tarihi sun bayyana cewa rubutun kur'anin yana komawa ne zuwa ga zamanin Khalifa na uku Usman bin Afan, domin kuwa kur'anin ba bubu li'irabi a cikinsa. Shamsuddin shi ne limamin masallacin, ya kuma bayyana cewa kabilarsu ita ce karamar kabila a cikin kasar, ta yadda yarensu ma ba a iya rubuta shi, amma kuma Allah ya ba su babbar falala ta rubutaccen fiyayyen kalami mai tsarki, wato alkur'ani mai girma. Saboda yawan amfani da aka yi da wannan kur'ani ya sanyatakardunsa sun fara rudiddigewa, wannan ya sanya aka ga akwai bukatar a sake gyara shi, saboda haka gwamnati kasar Chana ta aike da wasu kwararru kan gyara kayan tarihi zuwa yankin, amma al'ummar kauyen sun kai da fatan kan cewa dole ne gyaran wannan kur'ani ya kasance a cikin kauyen, an kwashe kimanin wata daya ana gyaran kur'anin. A cikin watan Ramadan al'ummar wannan kauye sukan gudanar da tarukan addinin a wannan masallaci mai tsawon tarihi, inda har wasu daga cikin mabiya addinin musulunci sukan zo daga wasu yankuna da ke cikin kasar Chana, sukan halarci tarukan addini da ake gudanarwa a wannan masallaci mai tsawon tarihi.
402400