IQNA

Za A Gudanar Da Zama Kan Tattalin Arzikin Kasashen Musulmi A Moris

16:01 - May 11, 2009
Lambar Labari: 1777018
Bangaren kasa da kasa: A mako mai zuwa ne za a gudanar da zama kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a tsibirin Moris.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Afriquejet cewa; A mako mai zuwa ne za a gudanar da zama kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a tsibirin Moris. Rahoton ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da zaman taron dai ita ce kara fadada harkokin kasuwanci da saka hannayen jari a kamfanonin kasashen musulmi, domin kara karfafa harkar kasuwar hannayen jari daidai da shari'ar musulunci. Za a gudanar da taron a babban ginin bankin kasa na Moris. Taron zai samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki sama da 200, da suka hada da shugabannin bankuna da manyan 'yan kasuwa gami da malaman jami'a daga sassa daban-daban na kasashen musulmi. Shugaban bankin kasar Moris ya bayyana cewa an zabi kasarsa ne domin gudanar da wannan taro mai matukar muhimmanci, saboda rawar da take takawa ta fuskacin harkokin tattalin arziki a matsayin kasar musulmi.


402595




captcha