Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro a birnin Shajah na kasar Hadaddiyar daular larabawa, dangane da matsalolin tattalin arziki da suka yi wa duniya katutu, da kuma mahangar musulunci kan hakan da yadda za a warware matsalolin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAM cewa; An gudanar da wani taro a birnin Shajah na kasar Hadaddiyar daular larabawa, dangane da matsalolin tattalin arziki da suka yi wa duniya katutu, da kuma mahangar musulunci kan hakan da yadda za a warware matsalolin. Taron wanda aka gudanar a jami'ar birnin Sharjah ya samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki daga kasashen larabawa da na musulmi, gami da wasu masana daga nahiyar turai, inda aka tattauna muhimman matsaloli da duniya ke fuskanta ta fuskacin tattalin arziki, da kuma bayyana mahangar musulunci kan hakan gami da hanyoyin da za a bi wajen shawo kan wannan matsala. Mahalarta taron sun gabatar da jawabai da makaloli.
402638