IQNA

Mutanen Jamus Ba Su Amince Da Gudanar Da Taron Nuna Kyama Ga Musulunci Ba

Bangaren kasa da kasa: Daruruwan mutanen kasar Jamus da suka hada da mabiya addinain musulunci da kuma kiristoci sun gudanar da gangami a garuruwa daban-daban na kasar, domin nuna rashin amincewarsu da taron da wasu masu tsananin gaba da addinin musulunci za su gudanar a karo na biyu a birnin Kolien na nuna kyama ga addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islam Alyaum cewa; Daruruwan mutanen kasar Jamus da suka hada da mabiya addinain musulunci da kuma kiristoci sun gudanar da gangami a garuruwa daban-daban na kasar, domin nuna rashin amincewarsu da taron da wasu masu tsananin gaba da addinin musulunci za su gudanar a karo na biyu a birnin Kolien na nuna kyama ga addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin mabiya addinin kirista da suka hada da 'yan siyasa da 'yan majalisar dokokin kasar gami da musulmi sun gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar wasu masu tsananin gaba da addinin musulunci da ke neman gudanar da taro karo na biyu, domin nuna kyama ga addinin musulunci da musulmi.

402603