IQNA

Dangantaka Tsakanin Musulunci Da Kiristanci A Karni Na 21

15:23 - May 12, 2009
Lambar Labari: 1777503
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro na kasa da kasa kan danganataka tsakanin addinan musulunci da na kiristanci a cikin karni na 21, a cibiyar bincike kan addinai da ke birnin Pasadina na kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Labanan ta Almutaqbal cewa; An gudanar da wani taro na kasa da kasa kan danganataka tsakanin addinan musulunci da na kiristanci a cikin karni na 21, a cibiyar bincike kan addinai da ke birnin Pasadina na kasar Amurka. Rahoton ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar masana da marubuta na kasar Amurka da ma wasu kasashen ketare, da suka hada da mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kiristanci. Mahalrta taron sun tattauna dangane da yadda yanayin da dukkanin mabiya addinan suke ciki a kasashen da suke su ne marassa rinjaye, da kuma yadda ya kamata hakkokin kowane bangare a kiyaye su. Babban abin da mahalrta taron suka kara karfafa maganganusu a kansa shi ne, samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinan biyu a kowane lokaci, tare da tattaunawa domin warware kowace matsala da ka iya tasowa tsakaninsu.


403366







captcha