Bangaren kasa da kasa: Wakilai na mabiya addinai da aka safkar daga sama na gudanar da wani taro a birnin Brussel na kasar Belgium kan matsalolin harkokin tattalin arziki da suka addabi kasashen duniya, tare da bijiro da mahangar addinai wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; Wakilai na mabiya addinai da aka safkar daga sama na gudanar da wani taro a birnin Brussel na kasar Belgium kan matsalolin harkokin tattalin arziki da suka addabi kasashen duniya, tare da bijiro da mahangar addinai wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki. Wannan dai karo na shida ake gudanar da irin wannan taro, an gudanar da shi a karo na biyar a cikin shekara ta 2005. Yanzu haka dai taron na samu halartar wakilan mabiya addinai da aka safkar daga sama daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da wasu kasashen yammacin turai kamar su Holland, Faransa, Jamus, Birtaniya, Italia, Spain, Ireland, cheque Republic, Pilland, Swedeen, Danmaek, Romania, Rasha, da kuma mai masafkin baki Belgium.
403287