IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Hijabi A Birnin Ta'if Na Saudiyya

Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro kan muhimmancin hijabi a rayuwar mata a jami'ar musulunci da ke birnin Ta'if da ke kasar saudiyya, wanda aka baiwa take Hijabi gadon manzon Allah SAW.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Saudiyya Ukaz cewa; Za a gudanar da wani taro kan muhimmancin hijabi a rayuwar mata a jami'ar musulunci da ke birnin Ta'if da ke kasar saudiyya, wanda aka baiwa take Hijabi gadon manzon Allah SAW. Taron wanda cibiyar kula da harkokin mata da wayar da kansu kan koyarwar addinin musulunci ta kasar Saudiyya ta shirya, za a gudanar da shi ne a jami'ar musulunci da ke birnin Ta'if mai dogon tarihi, kuma zai samu halartar daliban jami'a daga sassa daban-daban na kasar Saudiyya. Wadda ta shirya gudanar da wannan taro Fatimah Judi ta bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce kara fadakar da mata kan muhimmancin da ke tattare da saka hijabin musulunci a cikin rayuwar mata ta zamantakewa, tare da kara karfafa gwiwarsu wajen kiyaye saka hijabin a kowane lokaci.




403274