Bangaren nazari: mai kula da taron kasa da kasa kan Karatun Digirin digirgiri na Mahdawi y ace an samu makaloli dari kan Mahdawiya.
Said Muhsin Musawi Nasab shugaban da ke kula da shirya taron kasa da kasa kan Mahdawiya a wata tattaunawa da bangaren nazari da bincike na cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa; a cikin gida a Iran an samu makaloli 64 da ke Magana da bayani kan Mahdawiya daga kuma ketare aka samu makaloli 47 kuma ya zuwa yanzu kuma sun gudanar da zama har sau uku da suka shafi Zuhuri, da dalilan hakan da kuma hanyoyin zuhurinsa.
404056