IQNA

Kungiyar OIC Ta Bukaci Isara'ila Da Ta Dakatar Da Yin Gine-Gine A Cikin Qods

23:06 - May 13, 2009
Lambar Labari: 1778182
Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan, a cikin wani sako da ya aike wa ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana cewa; muna bukatar gwamnatin Amurka da ta takawa Isra'ila birki kan ayyukan wuce gonad a iri da take aikatawa kan birnin Qods da al'ummar musulmi da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA cewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan, a cikin wani sako da ya aike wa ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana cewa; muna bukatar gwamnatin Amurka da ta takawa Isra'ila birki kan ayyukan wuce gonad a iri da take aikatawa kan birnin Qods da al'ummar musulmi da ke birnin. A cikin sakon ya kara da cewa Isra'ila tana aikata ayyuka da suka saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa a Qods, da hakan ya hada da batun gine-ginen da take yi a cikin masallacin Qods mai alfarma, da kuma rushe gidajen palastinawa mazauna birnin, da nufin mayar da birnin na yahudawa kawai, ya ce wannan ya yi karo da dukkanin ka'idoji da dokoki na kasa da kasa, kuma nauyi da ya rataya kan Amurka da ta taka wa gwamnatin yahudawan birki.

403234



captcha