IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Mu'ujizar Lafazin Kur'ani A Gaza

23:05 - May 13, 2009
Lambar Labari: 1778183
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro kan mu'ujizar lafazin kur'ani a Gaza, tare da auna ma'anonin kalmomi da wasu na daban da ke cikin kur'ani, da yadda lafazinsu kan yi tasiri wajen bayar da wata ma'ana ta daban.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Ma'a cewa; An gudanar da wani taro kan mu'ujizar lafazin kur'ani a Gaza, tare da auna ma'anonin kalmomi da wasu na daban da ke cikin kur'ani, da yadda lafazinsu kan yi tasiri wajen bayar da wata ma'ana ta daban. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar masana daga yankuna daban-daban na zirin Gaza da kuma kasar Masar, da suka hada da makarnta da masu gudanar da nazari kan harkokin da suka shafi ilimin kur'ani. Mahalarta taron sun gabatar da jawabai daban-daban da kuma makaloli. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai da kuma makaloli har da Muhammad Sha'aban Alawan, wanda ya gabatar da wata makala kan ma'anar kalmar tsoro a cikin kur'ani mai tsarki.

403206


captcha