IQNA

Dole Ne Kalaman Pop Benedict Dangane Da Gaza A Gansu A Aikace

14:43 - May 14, 2009
Lambar Labari: 1778298
Bangaren kasa da kasa: Masanin nan musulmi dan kasar Switzerland Tarik Hasim ya bayyana cewa, maganganun da poproma Benedict na 16 ke yi kan neman kawo sulhu da zaman lafiya da kuma batun Gaza dole ne a gansu a aikace matukar dai dagaske yake yi kana bin da yake furtawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islamtoday cewa; Masanin nan musulmi dan kasar Switzerland kuma malamain jami'ar birnin Jenneva Tarik Hasim ya bayyana cewa, maganganun da poproma Benedict na 16 ke yi kan neman kawo sulhu da zaman lafiya da kuma batun Gaza dole ne a gansu a aikace matukar dai dagaske yake yi kana bin da yake furtawa.Tarik Ramadan ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da ta hada shi da jaridar kasar Italia La Stampa, ya ci gaba da cewa Benedict ya yi addu'a kan Allah ya kawo zaman lafiya da sulhu, lahali lamarin ba wai addu'a kawai yake bukata ba, a a yana bukatar tashi tsaye ne tare da yin aiki da gasket, ya ce a tafiyar da pop din zai yi zuwa palastinu ya kamata ya yi amfani da wannan damar wajen la'antar abin da Isra'ila ke yin a kasha fararen hula palastinawa da bas u da laifin tsaye ballantana na zaune.

404784



captcha