Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan tafiyar da harkokin kudi a musulunce jami'ar Jidda da ke kasar Saudiyya, tare da hadin gwiwa tsakanin jami'ar da kuma cibiyar kula da harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Saudi Gazzete cewa; Za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan tafiyar da harkokin kudi a musulunce jami'ar Jidda da ke kasar Saudiyya, tare da hadin gwiwa tsakanin jami'ar da kuma cibiyar kula da harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Labanan. Rahoton ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan shiri na bayar da horo kan harkokin kudi a musulunce dai ita ce, samar da cikakkiyar masaniya wajen tafiyar da harkokin bankunan kasashen musulumi daidai da koyarwa irin ta addinin musulunci, ta yadda za su kauce wa fadawa cikin wasu lamurra da babu natsuwa a cikinsu, tare da dogara da kai wajen bunkasa harkokinsu ba tare da dogara da wasu bankuna na waje ba, ta yadda ba za su fuskanci barazanar rushewa ba ko da a can gaba.
404605