Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Today Zaman cewa; Ana ci gaba da gudanar da taron harkokin tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Azmir na kasar Turkiya.Rahoton ya kara da cewa; Kwamitin kula da harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulumi ta OIC shi ne ya fara gudanar da zamansa a birnin Azmir na kasar Turkiya, wanda kuma wannan shi nekaro na ashirin da biyar da wannan kwamiti ke gudanar da babban zamansa. Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin ya fara gudanar da babban zaman nasa ne a katafaren otel din nan na birnin Azmir, wanda zaman taron kuma yana samun halartar ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya, da kuma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo, gami da wakilan kasashen muslumi mambobi a kungiyar.
404494