IQNA

Za A Kai Karar Malaman Saudiyya Da Ke Kafirta Tare Da Halasta Jinin Shi'a

Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da yada ilimin iyalan gidan manzon Allah da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki da kuma birnin Alkahira na kasar Masar, na shirin kai karar malaman Saudiyya da ke kafirta tare da halasta jinin mabiya mazhabar shi'a a kotun manyan laifuka ta duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga tashar talabijin ta Rasid cewa; Shugaban cibiyar Alul baiti AS da ke birnin Alkahira na kasar Masar Muhammad Duraini, da kuma babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Wa'ad Hossaini, sun fitar da wani bayani na bai daya da ke cewa; cibiyoyinsu na shirin kai karar wasu malaman kasar Saudiyya su 22 da suka fitar da fatawoyi na kafirta duk wani mabiyin mazhabar shi'a, tare da halasta jininsa, kuma karar za a kai tan e a gaban kotun manyan laifuka ta duniya domin su fuskanci hukunci. Wa'ad Hosseini ya bayyana cewa yanzu haka an shirya kararrakin kuma za a mika su ga kotun manyan laifuka ta duniya, ya kara da cewa malaman wahabiyawa da 'yan salafiya suna kara karfafa gwiwar mabiyansu ne da wadannan fatawowi na kiyayya da iyalan gidan manzon Allah da mabiyansu a ko'ina suke cikin fadin duniya.

404479