IQNA

Kafa Dalili Da Kur'ani A Mahangar Allamah Tabataba'i

14:39 - May 14, 2009
Lambar Labari: 1778307
Bangaren kasa da kasa: Littafin nan mai suna kafa dalili da ayoyin kur'ani a mahangar Allamah Sayyid Tabataba'I da marubucin nan na kasar Labanan Sheikh Shebr Fakih ya rubuta a cikin shafuka 346, an baje kolinsa a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani daya daga cikin masu madaba'antu da suka kawo littafansu a kasuwar baje kolin Tehran Ali Ru'aini, ya bayyana cewa littafin nan mai suna kafa dalili da ayoyin kur'ani a mahangar Allamah Sayyid Tabataba'i da marubucin nan na kasar Labanan Sheikh Shebr Fakih ya rubuta a cikin shafuka 346, an baje kolinsa a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran. Ya ci gaba da cewa madaba'antar Darul Huda da ke birnin Beirut na kasar Labanan ita ce ta dauki nauyin buga wannan littafi mai matukar kima ta ilimi, kuma shi n ekaron farko da aka kawo wannan littafi a wajen kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda kuma wannan shi ne karo na 22 da ake gudanar da wannan kasuwar baje koli ta duniya a birnin Tehran.

404494






captcha