IQNA

Za A Gudanar da Wani Wasan Kwaikwayo A Iran Kan Gaza

Bangaren fasaha: Za a gudanar da wani wasan kwaikwayo mai take dukkanin asubahin duniya a Iran dangane da yanayin da al'ummar Gaza suke ciki, da kuma irin zaluncin da suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani shahararren marubucin wasan kwaikwayo na Iran Ayub Agakhani ya bayyana cewa; nan bad a jimawa ba za a gudanar da wani wasan kwaikwayo mai take dukkanin asubahin duniya a Iran dangane da yanayin da al'ummar Gaza suke ciki, da kuma irin zaluncin da suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya. Ya ci gaba da cewa suna fatan nan da makonni uku masu zuwa su fara gudanar da wannan wasan kwaikwayo, domin yanzu haka wadanda za su gudanar da wasan suna cikin yin rihasal ne. Ya ce babbar manufar shirya wannan wasan kwaikwayo ita ce bayyana asalin yahudawan sahyuniya da kuma munanan akidunsu na rashin imani da tausayi kan bil adama, da kuma yadda suke kallon sauran mutane wadanda ba yahudawa ba, wanda kuma hakan ya bayyana ta hanyar kisan kiyashin da suka yi kan al'ummar Gaza.

404767