Bangaren kasa da kasa: An kawo wasu daga cikin littafan fikihun shafi'iyya a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, daga ciki kuwa har da littafin nan mai suna fikihun shafi'iyya a saukake da kuma fikihu da ka'idojin tunani a zamanance.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An kawo wasu daga cikin littafan fikihun shafi'iyya a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, daga ciki kuwa har da littafin nan mai suna fikihun shafi'iyya a saukake da kuma fikihu da ka'idojin tunani a zamanance, wanda wannan littafi da fitaccen marubucin nan na kasar Syria kuma malamin jami'ar Demascus Dr. Zuhaili ya rubuta, ya yi bayani ne dangane da muhimmancin da ke tattare da yin amfani da ilimi da mahangar musulunci baki daya wajen rarrabe hukunce-hukuncen addini. A wani bangaren kuma ya yaba da yadda malamai suka yi amfani da fikira ta zamani wajen kafa tsarin musulunci a Iran, wanda ya yi daidai da tunani na islama da kuma koyarwar addini a zamanance. Da dama daga cikin littafan da aka baje kolinsu a wannan karo suna dauke ne da muhimman batutuwa na ilimi da suka danganci batuwa na ijtihadi ko kirkiro hukunci bisa dogaro da dalilai, musamman ma dai littafan fikihu daga cikinsu.
404121