IQNA

An Fara Bayar Da Horo Ga Malaman Kur'ani A Pakistan

14:55 - May 14, 2009
Lambar Labari: 1778314
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wani shiri na bayar da cikakken horo ga malaman da ke koyar da karatun kur'ani da harda a kasar Pakistan, wanda aka fara jiya a birnin Islama bad fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Pakistan cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da cikakken horo ga malaman da ke koyar da karatun kur'ani da harda a kasar Pakistan, wanda aka fara jiya a birnin Islama bad fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suke halartar wannan bayar da horo sun fit one daga cibiyoyin kur'ani daban-daban da ke kasar. Shugaban cibiyar karatun kur'ani ta birnin Islama bad Abrar Hossein shi ne ke jagorantar wannan bayar da horo da zai kwashe tsawon kawanaki uku jere ana gudanar da shi, an ware azuzuwa daban-daban ga masu halartar bayar da horon, suka hada da azuzuwan karatu da kuma ka'idojin karatun kur'ani wato tajwidi.

404013


captcha