Bangaren kasa da kasa: Babbar cibiyar bayar da agajin nan ta kasar Qatar ta kalubalanci gwamnatin Isla'ila kan ci gaba da yin gine-ginen da take yi a cikin harabar masallacin Qods mai alfarma, kamar yadda cibiyar ta fara gudanar da wasu shirye-shirye na ci gaba yin fito na fito da wannan mummunar manufa ta Isra'ila kan wurare masu tsarki da ke Qods.