IQNA

Za A Bude Hanyar Bayar Ta Fatawowin Musulunci Ta Wayar Tarho A Birtaniya

Bangaren kasa da kasa: Za a bude wata hanya mafi sauki wajen karbar fatawoyin musulunci a kasar Birtaniya ta hanyar wayar tarho, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a aiwatar da irin wannan shiri a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar sharq alausat cewa; Za a bude wata hanya mafi sauki wajen karbar fatawoyin musulunci a kasar Birtaniya ta hanyar wayar tarho, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a aiwatar da irin wannan shiri a kasar. Ta wannan hanya za a iya samun fatawowi daidai da hukunce-hukuncen musulunci, wadanda manyan malaman addinin musulunci suka tsara kan mas'aloli da dama da suka danganci rayuwa da mu'amala da kuma ibada. Za a rika karbar fatawowin ne a cikin harsuna daban-daban, da suka hada da harshen turanci, harshen larabci da harshen Urdu, wadanda sun e harsunan da musulmin kasar Birtaniya suka fi yin amfani da su. Za a rika karbar wasu kudade a kan dukkanin mintocin da mutum zai yi yana Magana, a kan kowane minti daya za a karbi kimanin dala daya ta Amurka.

403937