IQNA

An Yi Suka Kan Yawan Bayar Da Fatawowi Kan Kuskure A Tashoshin Larabawa

Bangren kasa da kasa: Tashoshin larabawa da ke watsa shirye-shiryensu kan tauraron dan adam musamman ma wadanda ke yada shirye-shirye na addini, sukan bayar da fatawowi kan kurakurai da wuce gonad a iri da sunan musulunci, dole ne a shawo kan lamarin da hanyar daidaita dukkanin shirye-shirye da ake watsawa kan tauraron dan adam da sunan addinin musulunci su yi daidai da koyarwa irin ta addinin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar The National cewa; Babban daraktan tashar talabijin din kasar Saudiyya ta Almajd Fahad Shamshiri ya bayyana cewa; Tashoshin larabawa da ke watsa shirye-shiryensu kan tauraron dan adam musamman ma wadanda ke yada shirye-shirye na addini, sukan bayar da fatawowi kan kurakurai da wuce gonad a iri da sunan musulunci, dole ne a shawo kan lamarin da hanyar daidaita dukkanin shirye-shirye da ake watsawa kan tauraron dan adam da sunan addinin musulunci su yi daidai da koyarwa irin ta addinin. Ya ci gaba da cewa wannan lamari ne mai matukar hadari, kuma idan ba a dauki matakan gaggawa wajen shawo kan wannan lamari ba, zai jawo illa mai girma ga musulunci da musulmi a duniya.

403881