IQNA

Cibiyar Yada Fikirar Musulunci Ta Kai Kayyakinta A Baje Kolin Littafai Na Tehran

Bangaren kasa da kasa: Cibiyar yada tunanin da al'adun musulunci ta kasar Labanan ta baje kolin kayayyakinta a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda kuma wannan shi ne karo na ashirin da biyu da ake gudanar da wannan kasuwar baje koli a birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya zanta da Balal Amis wanda ya bayyana cewa; Cibiyar yada tunanin da al'adun musulunci ta kasar Labanan ta baje kolin kayayyakinta a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda kuma wannan shi ne karo na ashirin da biyu da ake gudanar da wannan kasuwar baje koli a birnin. A cikin zantawar wadda ta hada daraktan kula da harkokin watsa kayayyakin cibiyar zuwa kasashen duniya Balal Amis, ya bayyana cewa yanzu haka akwai wasu daga cikin irin kayayyakin da cibiyar take samarwa domin domin yada tunani da bayyana wa duniya ci gaban musulunci da aka kawo a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a nan birnin Tehran. Y ace daga ciki kuwa hard a wasu littafai da suka hada da kur'anai da dai sauransu.

403604