IQNA

Kwamitin Harkokin Kasuwanci Na OIC Ya Fara Gudanar Da Zamansa

14:52 - May 14, 2009
Lambar Labari: 1778323
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin kula da harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulumi ta OIC ya fara gudanar da zamansa a birnin Azmir na kasar Turkiya, wanda kuma wannan shi nekaro na ashirin da biyar da wannan kwamiti ke gudanar da babban zamansa.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Turkiya cewa; Kwamitin kula da harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulumi ta OIC ya fara gudanar da zamansa a birnin Azmir na kasar Turkiya, wanda kuma wannan shi nekaro na ashirin da biyar da wannan kwamiti ke gudanar da babban zamansa. Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin ya fara gudanar da babban zaman nasa ne a katafaren otel din nan na birnin Azmir, wanda zaman taron kuma yana samun halartar ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya, da kuma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo, gami da wakilan kasashen muslumi mambobi a kungiyar.

403883



captcha