IQNA

An Bude Wasu Cibiyoyin Kur'ani Biyu A Birnin Karbala

15:22 - May 16, 2009
Lambar Labari: 1778970
Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin manyan malaman kasar Iraki Ayatollah Mohammad taqi Modarrisi ya bude wasu manyan cibiyoyin harkokin kur'ani a birnin Karbala mai alfarma da ke kudancin kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran iba cewa; Daya daga cikin manyan malaman kasar Iraki Ayatollah Mohammad taqi Modarrisi ya bude wasu manyan cibiyoyin harkokin kur'ani a birnin Karbala mai alfarma da ke kudancin kasar Iraki. Rahoton ya ci gaba da cewa an bude wadannan cibiyoyi biyu ne da aka bai wa suna mu'assasar Sayyidah Rukayyah, da kuma mu'assasar Sayyid Aba Abdillah Alhossain AS. Babban makasudin bude cibiyoyin shi ne samara da wata hanya ta koyar da karatun kur'ani ga kanan yara da kuma matasa, ta yadda za su samu tarbiya irin ta kur'ani da koyarwar addinin musulunci. Haka nan kuma cibiyoyin biyu za su rika koyar da yarukan larabaci da turanci gami da faransanci.

405386



captcha