Bangaren kasa da kasa: Kwamitin hadin gwiwa tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista domin kare masallacin Qods da sauran wurare masu tsarki da ke birnin, ya kirayi Pop Benedict na 16 da ya dauki matakan da suka dace a aikace domin kare Qods da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birnin mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam cewa; Kwamitin hadin gwiwa tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista domin kare masallacin Qods da sauran wurare masu tsarki da ke birnin, ya kirayi Pop Benedict na 16 da ya dauki matakan da suka dace a aikace domin kare Qods da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birnin mai alfarma. A nasa bangaren masanin nan musulmi dan kasar Switzerland kuma malamain jami'ar birnin Jenneva Tarik Hasim ya bayyana cewa, maganganun da poproma Benedict na 16 ke yi kan neman kawo sulhu da zaman lafiya da kuma batun Gaza dole ne a gansu a aikace matukar dai dagaske yake yi kana bin da yake furtawa.Tarik Ramadan ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da ta hada shi da jaridar kasar Italia La Stampa, ya ci gaba da cewa Benedict ya yi addu'a kan Allah ya kawo zaman lafiya da sulhu, lahali lamarin ba wai addu'a kawai yake bukata ba, a a yana bukatar tashi tsaye ne tare da yin aiki da gasket, ya ce a tafiyar da pop din zai yi zuwa palastinu ya kamata ya yi amfani da wannan damar wajen la'antar abin da Isra'ila ke yin a kasha fararen hula palastinawa da bas u da laifin tsaye ballantana na zaune.
405378