IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Shubhohin Yammacin Turai Dangane Da Ma'aiki SAW

Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya domin yin dubi dangane da shubhohin da yammacin turai ke kawowa kan manzon Allah SAW, tare da fitar da hanyoyin mayar musu da martani.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Aljazira da ake bugawa a kasar saudiyya cewa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya domin yin dubi dangane da shubhohin da yammacin turai ke kawowa kan manzon Allah SAW, tare da fitar da hanyoyin mayar musu da martani. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai samu halartar malamai dam asana gami da malaman jami'oi daga kasashen musulmi daban-daban, domin daukar mataki na bai daya wajen mayar da martini kan abubuwan da kasashen yammacin turai suke kirkira suna dangantawa da manzon Allah SAW, da nufin bata fuskar addinin musulunci da kuma sakon da yake dauke da shi a idon duniya.

403446